An kama Faston da ya cire zuciyar yarinya a Kalaba
A Kurosriba, ’yan sanda sun kama wani Fasto mai suna Tony Obo da ke layin Okon Edak, inda aka zarge shi da cire zuciyar wata yarinya ’yar shekara daya da haihuwa, mai suna Success Ime. A yayin bincike, ’yan sanda sun samu zuciyar a hannunsa, inda aka yi zargin cewa zai yi tsafi da ita […]
A Kurosriba, ’yan sanda sun kama wani Fasto mai suna Tony Obo da ke layin Okon Edak, inda aka zarge shi da cire zuciyar wata yarinya ’yar shekara daya da haihuwa, mai suna Success Ime.
A yayin bincike, ’yan sanda sun samu zuciyar a hannunsa, inda aka yi zargin cewa zai yi tsafi da ita ne a harabar cocin nasa. Bayan an kama shi, an gano wasu tarkace da ya yi tsafi dasu a wannan majami’a, wadanda suka hada da kawunan awakai, sassan jikin namiji da mace da kuma karin wasu tarkacen.
Kakar yarinyar da aka cire wa zuciyar, mai suna Arit Ime, ta shaida wa Aminiya cewa: “Jiya da talatainin dare muka ji ana buga mana kofar daki, daga nan ne fa muka ga wasu mutum biyu lullube da fuska, suka kutsa kai cikin dakinmu da ke lamba 8 layin Okon Edak. Shigar su ke da wuya dakin namu sai suka fara bincike ko’ina, bayan sun umarce mu da mu kwanta rub da ciki mu rufe idanuwanmu, idan kuma mun ki za su harbe mu. A zatonmu ’yan fashi ne, ashe ba mu sani ba sun zo kama jikata ne.”
Wakilinmu ya tambayi Arit yadda aka gano cewa wannan Fasto ne ya sanya aka zo aka dauki jikar tata. Sai ta ci gaba da cewa: “Bayan sun tafi da yarinyar ne muka rika yin ihu a kawo mana dauki. Shi ne fa sai makwabta suka garzayo har aka yi sa’ar cafke daya daga cikinsu tare da kokarin matasan unguwa ’yan sintiri, su kuma sai suka buga wa ’yan sanda waya suka zo.”
Ta ci gaba da cewa: “Labarin yadda aka gano wasu tarkace da suturar da jikata ta sanya lokacin da aka sace ta ne ya sanya muka tabbatar jikata ce.”
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba, Irene Ugbo ta tabbatar da kama Faston tare da wasu mutum shida. Ta ce za a tuhume shi da laifin aikata kisan kai kana kuma ragowar abokan mu’amalarsa, su ma rundunar za ta bazama nemansu.