An kama faston da ya yi garkuwa da kansa a Kaduna

Dubun wani fasto mai suna James Clement ta cika bayan da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta kama shi saboda yin karyar an yi garkuwa da shi. A cewar rundunar wanda ake zargin tare da abokin hadin bakinsa mai suna George Otokpa sun nemi ’yan uwan Fasto Clement su biya diyyar Naira miliyan biyar kan […]

An kama faston da ya yi garkuwa da kansa a Kaduna
An kama faston da ya yi garkuwa da kansa a Kaduna

Dubun wani fasto mai suna James Clement ta cika bayan da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta kama shi saboda yin karyar an yi garkuwa da shi.

A cewar rundunar wanda ake zargin tare da abokin hadin bakinsa mai suna George Otokpa sun nemi ’yan uwan Fasto Clement su biya diyyar Naira miliyan biyar kan an yi garkuwa da shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo ne ya sanar da haka a wata sanarwa a shekaranjiya Laraba.

Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane na Rundunar ne ya gano inda Fasto Clement ke boye. “Wanda ake zargi Clement an gano inda yake boye ne bayan ’yan uwansa biyu sun sanar da ’yan sanda cewa an sace shi. Da aka bibiyi lambarsa sai aka gano inda yake boye tare da abokin aikata laifinsa, George Otokpa mai shekara 22. Sun bukaci ’yan uwan Faston su biya Naira miliyan biyar a matsayin fansa. Saboda haka da zarar an kammala bincike za a tura su kotu,” inji shi.

Sanarwar ta ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umar M. Muri ya yi Allah wadai da irin wannan rashin imani, inda ya shawarci al’umma su  kauce wa aikata irin wannan rashin tausayi ga ’yan uwansu.