An kama Fulani 4 da yunkurin sace wani sarki a Oyo

Rundunar ’yan sandan kwanton bauna a Jihar Oyo ta kama wasu Fulani 4 da suka yi yunkurin sace wani sarki domin yin garkuwa da neman fansar kudi daga fadarsa. Asirinsu ya tonu ne a lokacin da biyu daga cikinsu suka isa fadar sarkin domin tsara dabarun yadda za su sace shi, inda a nan take […]

An kama Fulani 4 da yunkurin sace wani sarki a Oyo
An kama Fulani 4 da yunkurin sace wani sarki a Oyo

Rundunar ’yan sandan kwanton bauna a Jihar Oyo ta kama wasu Fulani 4 da suka yi yunkurin sace wani sarki domin yin garkuwa da neman fansar kudi daga fadarsa.

Asirinsu ya tonu ne a lokacin da biyu daga cikinsu suka isa fadar sarkin domin tsara dabarun yadda za su sace shi, inda a nan take ’yan sanda suka kama su.
Da yake nuna wadannan mutane ga taron ’yan jarida a ranar Talata da ta gabata a ofishinsa da ke Ibadan, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammad Musa Katsina ya ce mutane 2 da aka fara kamawa a harabar fadar sarkin (da aka boye sunansa) su ne suka yi bayanin da ya kai ga kama sauran abokan huldarsu su 2 a maboyarsu. daya daga cikinsu mai suna Bolaji, ya sulale da ake nemansa ruwa a jallo. Duka wadannan Fulani masu suna Babatunde Ibrahim da Yusuf Abdullahi da Isa Abiodun da Alabi Azeez, suna zaune ne a garin Balugu cikin Jihar Kwara.
Bincike ya nuna cewa mako 3 da wucewa ke nan da wadannan mutane suka sace wani mutum mai suna Mista Arande da ke zaune a garin Omu-Aran a Jihar Kwara, suka karbi kudin fansa Naira miliyan 8 kafin su sallamo shi daga inda suka yi garkuwa da shi.
Kwamishinan ya ce, an samu makamai da kananan motoci guda 4 masu tsada da barayin suka saya daga cikin kubin fansar da suka raba a tsakaninsu kuma an gano shanu guda 15 da suka sace daga hannun makiyaya a tsakanin jihohin Kwara da Ekiti da Oyo.
Dangane da halin da wannan sarkin yake ciki sai Kwamishinan ya ce har zuwa lokacin da yake zantawa da ’yan jarida, sarkin bai samu labarin yunkurin sace shi ba. Ya ce: “Labarin da muka samu daga wata kafa ne ya sa na hanzarta aikewa da yarana cikin farin kaya da suka fara kama mutum biyu kafin su kai ga aikata danyen aikin nasu a fadar wannan sarki da ya tsallake rijiya da baya.” Kwamishinan ya yaba da irin hadin kai da rundunarsa take samu daga wasu mutane da suke taimaka masu da labaran bullar miyagun mutane da ake karya lagonsu kafin su aikata danyen aikinsu da kama su bayan sun aikata.
Har ila yau, ya nuna wa ’yan jarida wasu mutane 4 masu suna Mumuni Iyiola da Ayobanmi Adedeji da Lanre Olaminjuwon da Kareem Isiaka da aka kama su da raguna guda 20 da suka sace a Ibadan. Su kuwa Ahmed Lawal da Ojo Isiah, an same su ne da kananan motoci guda 3 da bindigar da suke yin amfani da ita wajen yin fashi da makami.