An kama fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Oyo
An kama gudaddun fursunonin a wasu kauyukan Jihar Osun.
’Yan sanda a Jihar Osun sun kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere bayan harin bom da aka kai gidan yarin Abolongo, inda suke tsere a Jihar Oyo.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Osun ta ce ta kama mutum 13 daga cikin fursununoin ne a wasu kauyuka na Karamar Hukumar Ejibo ta jihar.
- Buhari zai je taron zuba jari a Saudiyya, ya yi Umrah
- Lalata da dalibai: Poly Bauchi ta kori malamai daga aiki
Kakakin Rundunar, Yemisi Opalola ta ce kauyukan da ke kama gudaddun fursunonin na kan iyakar jihar Osun ne da Jihar Oyo.
A cewarta, an mika gudaddun fursunonin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar, kafin daga baya a mayar da su ga gidan yarin da suka gudo.
Yemisi ta ce wadanda aka kama din sun hada da Adekanbi Kola, Semiu Sali, Garuba Nurudeen, Ismaila Garuba, Nasifi Garuba, da Qadri Yusuf.
Sauran su ne Ezekiel Owolabi, Bamidele Kehinde, Daodu Emmanuel, Dele Babatunde, Adeyemo Ifalowo, Ridwan Akinsola da kuma Sola Owolabi.