An kama Hakimi kan zargin yi wa yarinya mai shekara 5 fyade a Gombe

Yanzu haka dai Hakimin na hannun ‘yan sanda

An kama Hakimi kan zargin yi wa yarinya mai shekara 5 fyade a Gombe

Fyade

Jamian tsaro sun kama wani Hakimin a Jihar Gombe, bisa zarginsa da yi wa wata karamar yarinya fyade.

Dubun basaraken ta cika ne bayan an zarge shi da yi wa yarinyar mai shekara biyar fyade a ranar Asabar din da ta gabata.

Al’ummar yankin dai na kokawa kan yawaitar faruwar irin wannan laifi a yankin da ake samu daga iyayen kasa kuma ake boyewa ba a fitarwa.

Tuni dai wasu rahotanni daga garin ke cewa an tube rawanin Hakimin tun bayan samun sa da wannan laifin, amma wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta a garin na Dukku ta tabbatar wa da wakilin mu faruwar lamarin.

Sai dai a majiyar ta ce ba a sauke Hakimin ba, domin Gwamna ne kadai ke da ikon sauke shi.

Sai dai iyayen yarinyar sun bukaci mahukunta da su bi musu kadin ’yar tasu da aka ci wa zarafin sannan aka lalata wa rayuwa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Oqua Etim, ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin sannan shi kuma Hakimin a ci gaba da tsare shi a ofishin ’yan sanda.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna