An kama hauren giwa na Naira miliyan 490 a Legas
Jami’an Hukumar Kwastam a Legas sun kama wani dan kasar China da suke zargi da mallakar hauren giwa da sassan jikin dabbar Pengolin masu nauyin kilo 2,344 da kudinsu ya haura Naira miliyan 490. Da yake nuna wa ’yan jarida buhunan kayayyakin, Kwamandan Hukumar Kwastam ta FOU da ke Ikeja, Legas, Kwanturola Muhammed Uba Garba […]
Jami’an Hukumar Kwastam a Legas sun kama wani dan kasar China da suke zargi da mallakar hauren giwa da sassan jikin dabbar Pengolin masu nauyin kilo 2,344 da kudinsu ya haura Naira miliyan 490.
Da yake nuna wa ’yan jarida buhunan kayayyakin, Kwamandan Hukumar Kwastam ta FOU da ke Ikeja, Legas, Kwanturola Muhammed Uba Garba ya ce, kasashen duniya ciki har da Najeriya sun haramta kashe wadannan dabbobi da cinikin sassan jikinsu domin guje wa karewarsu a duniya.
Ya ce sun yi nasarar dakile fasa kwaurin kayayyakin zuwa kasar China da kama dan Chinan da mai gadin gidan da aka boye kayayyakin ne a Legas bayan samun labarin sirri daga wadansu masu kishin kasa.
“Jariran dabbar Pangolin da fatunsu da jininsu, ana yin amfani da su a kasar China wajen hada magungunan gargajiya da tsafe-tsafe da sarrafa wasu abubuwa da suke sayarwa da tsada ga mabukata a China wacce ita ma ta kafa dokar hana kashe wadannan dabbobi da cinikinsu,” inji shi.
Kwanturola M.U. Garba wanda ya mika kayayyakin ga jami’in Hukumar Kula da Muhalli da Dabbobi ta kasa (NESREA), domin lalata su bayan kammala bincike, ya kuma nuna tarin buhunan shinkafa da motocin alfarma da kayan gwanjo da tayoyin mota da aikinsu ya kare da jarkokin man girki da buhunan tabar wiwi da kudinsu ya haura Naira biliyan daya da hukumar ta kama cikin wata daya.
Ya ce sakamakon dokar hana shigowa da shinkafa da gwamnati ta kafa, “An samu raguwar kama shinkafar a watan Fabrairu idan aka kwatanta da buhunan da aka kama a watan Janairu. Wannan ya biyo bayan tsaurara matakan tsaro da muka dauka ne a sassan jihohin Kudu maso Yamma, musamman a kan iyakokin kasa da tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama. Za mu ci gaba da tsaurara matakan tsaro a wadannan wurare domin ganin jama’a sun rungumi amfani da shinkafar gida, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyuka ga matasa da bunkasa tattalin arzikin kasar nan,” inji shi.