An kama hedimasta kan sayar da kujerun makaranta a Kano

An kama hedimastan ne a yayin da yake shirin sayar da kayan makarantar ta karkashin kasa

An kama hedimasta kan sayar da kujerun makaranta a Kano

Hedimastan Makarantar Firamaren Gaidar Makada da ke Jihar Kano ya shiga hannu kan sayar da kujeru da wasu kayayyakin makarantar ta bayan fage.

Hukumar Karbar Korafi da kuma yaki da Rashawa ta Jihar Kano ce ta kama hedimastan makarantar da ke Karamar Hukumar Kumbotso kan wannan badakalar.

Mai magana da yawun hukumar, Kabir Abba Kabir, ya ce an kama hedimastan ne bayan da aka gano wani shirin sayar da kayan makarantar ta karkashin kasa.

Kabir ya sanar a ranar Asabar cewa a sakamakon haka ne hukumar ta gudanar da bincike kan lamarin kuma tana kokarin kwato kayan makarantar da hedimastan ya sayar.

A cewar jami’in, “bincike ya gano wasu muhimman kayan makarantar da aka sayar, irin su karafa da kujeru da bencina da sauransu, wadanda suka yi layar zana a makarantar.

“Hedimastan makarantar ne ake zargi sakamkon kumbiya-kumbiya da aka gano aka kuma gabatar a lokacin zaman hukumar kula da makarantu da kuma shugabannin kungiyar iyaye da malamai.

“A yau (31 ga watan Agusta, 2024) aka kawo mana kara a hukumace, muka nan take muka dauki mataki.

“Hukumarmu ta dukufa wajen kwato kayan daga hannun wadanda suka saye su, da kuma tabbatar da tsaftace bangaren ilimin jihar Kano nan daga ayyukan bara-gurbi.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato