An kama iyayen da suka kashe jaririyarsu
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano ta kama wata amarya a Unguwar Rijiyar Lemo bisa zarginta da kashe jaririyarta bayan kwana uku da haihuwarta. Rahotanni sun ce amaryar mai suna Fa’iza Haruna mai kimanin shekara 17 ta kashe jaririyarta ce ta hanyar murde mata wuya daga bisani ta sanar da mijinta abin […]
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano ta kama wata amarya a Unguwar Rijiyar Lemo bisa zarginta da kashe jaririyarta bayan kwana uku da haihuwarta.
Rahotanni sun ce amaryar mai suna Fa’iza Haruna mai kimanin shekara 17 ta kashe jaririyarta ce ta hanyar murde mata wuya daga bisani ta sanar da mijinta abin da ta aikata shi kuma ya je ya binne jaririyar.
Asirin ango da amaryar ya tonu ne a lokacin da al’ummar unguwar suka ga iyayen sun dawo daga asibiti babu jaririyar inda suka yi hanzarin sanar da hukumar Hisba.
Kwamandan Hisba na yankin Fagge, Ustaz Salisu Umar ya shaida wa Aminiya cewa “Jama’ar unguwar ne suka yi zargin cewa iyayen jaririyar kashe ta suka yi sakamakon dawowa da suka yi daga asibiti ba tare da ita ba. Dama tunda aka haifi jaririyar sai uwarta take ta gaya wa jama’a cewa wai jaririyar ba ta da lafiya inda su kuma makwabtan suka shawarce ta kan ta kai ta asibiti. To bayan sun kashe ta sai suka yi amfani da wannan dama suka dauki gawar jaririyar zuwa asibiti, inda daga nan suka je suka binne ta suka dawo abinsu.” Kwamandan ya ce sun mika wadanda ake zargin ga Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano.
Mahaifiyar jaririyar Fa’iza Haruna ta ce ta dauki wannan mataki ne domin ta guje wa abin kunya kasancewar ta samu cikin jaririyar tun ba su yi aure ba. “kaddara ce ta sa mijinna ya yi min ciki tun ba mu kai ga aure ba, ni kuma don gudun jin kunyar jama’a ganin cewa watanmu biyu da aure ya sa na dauki wannan mataki. Amma na yi da-na-sanin aikata hakan,” inji ta.
Fa’iza ta ce, “Ban yi amfani da kowane makami wajen kisanta ba, da na shiga daki ne sai na murde mata wuya sai da ta mutu, koda yake dama can ba ta da cikakkiyar lafiya.”
Mijinta Mustapha Aminu mai shekara 29 ya ce ba ya da hannu a kisan jaririyar tasu domin ba ya gida a lokacin da matarsa ta yi wannan aika-aikar. “Lokacin ba na gida ta kashe jaririyar sai da na dawo ta gaya min, hakan ya sa na dauki gawar jaririyar na je na binne,” inji shi.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya ce tunda matar da mijin sun amsa laifinsu na kisan jaririyar za su gurfanar da su gaban kotu don hukunta su.