An kama iyayen da suka kulle dansu shekara 15
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da cafke kishiyar mahaifiyar mutumin da aka ceto daga kullen da aka yi masa na shekara 15 a Kano tare da mijinta, Malam Lawan Sheka. Ana zargin matar mai zama a Sheka Unguwar Fulani da hada baki da mijinta wajen kulle Ibrahim Lawan mai shekara 35 ba tare […]
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da cafke kishiyar mahaifiyar mutumin da aka ceto daga kullen da aka yi masa na shekara 15 a Kano tare da mijinta, Malam Lawan Sheka.
Ana zargin matar mai zama a Sheka Unguwar Fulani da hada baki da mijinta wajen kulle Ibrahim Lawan mai shekara 35 ba tare da barinsa ya fito ko kofar daki ba.
Kakakin Rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce ana zargin mutanen da daure mutumin ba tare da ba shi cikakken abinci da kulawar lafiya ba.
Kiyawa ya kuma tabbatar da cewa matashin na can kwance yana samun kulawa ta musamman a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Kakakin ya ce tuni Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Habu Sani ya umarci a kai batun gaban Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin zurfafa bincike
Yadda lamarin ya faru
A ranar Lahadi da ta gabata ne ‘yan sanda a jihar suka tabbatar da ceto matashin mazaunin unguwar Sheka dake cikin brinin Kano bayan samun rahoto cewa kishiyar uwar matashin ta hada kai da mijinta wanda kuma shi ne mahaifinsa suka kulle shi a daki tsawon shekaru 15.
Jami’an lafiya na sashen rundunar tsaro ta Operation ‘Kan ka ce kwabo’ ce dai ta jagoranci ceto mutumin.
Rahotanni sun nuna cewa mahaifin matashin, Malam Lawan Sheka limamin wani masallacin Juma’a ne.
Kamar Ibrahim, kamar Ahmad
Idan dai za a iya tunawa, ko a ranar Juma’ar da ta gabata sai da rundunar ’yan sandan ta ceto wani matashin mai kimanin shekaru 32 mai suna Ahmad Aminu a unguwar Farawa da ke Karamar Hukumar Kumbotso a birnin Kano.
Shi dai Ahmad an yi zargin an daure shi ne bisa zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi kusan tsawon shekaru bakwai, ko da yake daga baya ’yan sanda sun ce bincikensu ya nuna musu shekarun ba su kai haka ba.
Wata makwabciyar Ahmad din ce tun da farko ta kai korafi ga ’yan sanda kan halin da yake ciki, kafin daga bisani su kaddamar da bincike har su ka kai ga ceto shi.
Yanzu haka yana Asibitin Kwararru na Muratala Muhammad da ke Kanon inda ya ke samun kulawa.