An kama jagoran ’yan bindiga a kasuwa a Neja
An kama jagoran ’yan bindiga da ke addabar yankunan Jihar Neja a yayin da yake tsak da cin kasuwa…
’Yan sanda sun cafke wani jagoran ’yan bindiga mai suna Rabi’u Yusuf, wanda aka fi sani da Rabe, a babbar Kasuwar Tunga Mallam da ke Karamar Hukumar Paikoro a Jihar Neja.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Shawulu Ebenezer, ya ce jami’an rundunar sun cafke Rabe ne a yayin da ake tsaka da hada-hadar kasuwanci a babbar kasuwar.
Ya ce Rabe jagora ne a kungiyar ’yan bindiga ta ‘Mu Ware’ da ke addabar yankunan Beji, Maikunkele, Bosso, Gawu-Babangida, Sangeku, Bangi, Gulu, da kuma Lapai a jihar.
CP Shawulu Ebenezer ya ce, Rabe, wanda aka cafke a ranar 6 ga watan nan na Janairu bayan samun bayanan sirri, ya bayyana wa masu bincike hare-haren garkuwa da mutane da yake da hannu a ciki.
- Gawuna ya ɗauka zai ci banza kamar yadda Ganduje ya ci a 2019 — Kwankwaso
- Yadda mata ke fin maza ɗaukaka a finafinai a Nijeriya
Kwamishinan ya sanar da hakan ne a lokacin da yake gabatar da wasu masu laifi 14, cikinsu har da wasu mutum hudu da ake zargin sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20 suka karbi kudin fansa Naira miliyan 1.6.
Sauran sun hada da wadanda ake zargi da fashi da makami, fyade da kuma kisan gilla da dabacnci.