An kama jami’an asibiti masu saye da sayar da sassan jiki a Misra

Hukomomi a Misra sun sanar da cewa sun kama wasu gungun ma’aikatan kiwon lafiyar kasar bisa zargin harkallar saye da sayar da sassan jikin dan Adam a wani yanki mai suna Abu Nomros a Giza, Kudancin Misra, inda aka kama mutane 16, kamar yadda kafar yada labarai na Al Arabiya ta sanar. Wani jami’an tsaro […]

An kama jami’an asibiti masu saye da sayar da sassan jiki a Misra

Hukomomi a Misra sun sanar da cewa sun kama wasu gungun ma’aikatan kiwon lafiyar kasar bisa zargin harkallar saye da sayar da sassan jikin dan Adam a wani yanki mai suna Abu Nomros a Giza, Kudancin Misra, inda aka kama mutane 16, kamar yadda kafar yada labarai na Al Arabiya ta sanar.

Wani jami’an tsaro ya shaida wa Al Arabiya cewa masu laifin sun hada wani gungun mutane su 8, inda suke zuwa wajen wadanda suke da niyyar sayar da sassan jikinsu. Daga cikin gungun akwai likitan wani asibiti na Abu Al-Nomros, da ma’aikata a bangaren gwajin jini, inda suke sayen koda a matsayin Dala 1,400. Sai su sayar wa masu kudi Dala 25,000.

Mai magana da yawun Ma’aikatan Kiwon Lafiyan Misra, Dokta Khaled Mujahid, ya shaida wa Al Arabiya cewa a wannan harkallar ne a asibitin al-Shimi da ke birnin Abu al-Momros. Tuni aka kama wadanda ake zargi, kuma an fara bincike.

A daidai lokacin da ake bincike a kan lamarin, wata mata ta zo domin a mata dashen koda, sai aka sayo kodar daga wata mata a matsayin Dala 1130.

Jami’an tsaron sun kwace Dala 72,000 a asibitin. Bincike ya nuna wani mai suna Omar ne ya kawo matar da sayar da kodar ga matan da aka yi wa aikin. Da aka gabatar da bincike, sai Omar ya tabbatar da cewa matar ta sayar da kodar ta Dala 1130 da kuma sashen Hanta.

Wadda za ayi wad ashen, ta biya dala 25,000 wanda aka raba kamar haka: Dala 10,000 na likita wanda ake kira Izzat. Magungunan rage zafi kuma Dala 5,000, sai kuma masu kula da marasa lafiya (nas) Dala 1500, masu gwajin jina kuma Dala 3,000, sai sauran Dala 500 da za a ba wanda ya tsaya a tsakani.

Bincike ya nuna cewa daga cikin wadanda suke wannan harkallar akwai, likitoci masu kula da marasa lafiya (Nas) da masu tsayarwa a tsakani, an kama su da makudan kudi da ya kusa kai fam din Misra miliyan 1. Kuma suna da yawa, inda wasu ke zuwa kauyuka suna sayan gabban saboda rashin kudin da mutanen ke fama da shi. Sai likitocin su saya bayan sun gwada lafiyar gabban, sannan su sayar wa masu kudi da ke bukata.

Ma’aikatan Lafiyar kasar ta tabbatar da cewa ba a ba asibitin wannan damar ba, inda ma’aikatar ta tabbatar da cewa akwai ka’adojin irin wannan aikin a Misra.

ka’idar it ace dole wanda zai bayar sai ya yi rajista domin a tabbatar da cewa babu zargin harkallar safarar gabban jiki a ciki. Suma marasa lafiya sai sun samu shaidar yarda daga ma’aikatan lafiya domin a musu aiki.

Hukuncin safarar gabban jiki

Sashe na 18 na dokokin kasar ya nuna cewa duk wanda ya yi aiki ko ya taimaka wajen yin aikin day a yi sanadiyar mutuwar wanda ya bayar da gaba, shi ma za a mishi daurin rai-da-rai.

Sashe na 19 ya kara da bayanin cewa za a iya kashe mutum, ko daurin rai-da-rai ko kuma tara dab a zai gaza Fam miliyan 1 ba ko Fam miliyan 2 ga duk wanda ya cire wa wani wata gaba ta hanyar cuwa-cuwa domin ayi dashe.

Dokar kuma ta nuna cewa za a iya kwace lasisin asibitin da aka yi aikin na tsakanin shekara 3 zuwa 10. Sannan za a kwace lasisin aikin ma’aikatan da suka yi aikin.