An kama jami’an tsaro kan zargin sace Naira miliyan 40 a Gidan Gwamnatin Bayelsa
’Yan sanda uku da ma’aikatan Sibil Difens da wadansu ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bayelsa ne aka tsare sakamakon zarginsu da sace Naira miliyan 40 a ranar Larabar makon jiya. Bayanan da wakilin Aminiya ya samu daga jihar sun ce ana zargin wadanda aka kama su ne suka sace wancan makudan kudi, kuma yanzu haka suna […]
’Yan sanda uku da ma’aikatan Sibil Difens da wadansu ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bayelsa ne aka tsare sakamakon zarginsu da sace Naira miliyan 40 a ranar Larabar makon jiya.
Bayanan da wakilin Aminiya ya samu daga jihar sun ce ana zargin wadanda aka kama su ne suka sace wancan makudan kudi, kuma yanzu haka suna hedkwatar rundunar ’yan sandan jihar sashen binciken manyan laifuffuka (SCID). Bayanai sun ce ana tuhumar su daya-bayan daya.
Ma’aikatan suna aiki ne a ofishin Mataimakiyar Shugaban Ma’aikata ta Gidan Gwamnatin Uwargida Ebizi Ndiomu-Brown.
Majiyarmu ta ce an gano an sace kudin ne ranar Alhamis ta makon jiya lokacin da aka zo aiki aka iske an balle akwatunan ajiye kudin an kwashe ba tare da sanin ko wa ya aikata haka ba. Wata majiya da ke Gidan Gwamnatin ta yi zargin cewa babu yadda za a yi a ce kudin sun bata haka, ba tare da wani wanda ya san sirrin wurin ba.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Uche Anozia, ya bayyana matukar bacin ransa game da satar inda ya bayar da umarnin a kama duk jami’an tsaron da suke aiki a gidan.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa Mista Asinim Butswat game da mutanen da ake zargi musamman ’yan sanda da ma’akatan, inda ya tabbatar da cewa an kama su kuma ana gudanar da binciken kansu.
Mista Butswat, ya kara da cewa “Ayarin jami’an ’yan sanda da suka kware wajen gudanar da bincike sun ziyarci ofishin da aka yi satar a gidan gwamnatin sun ce tabbas an balle kofar ofishin amma kudin da ka sace Naira Naira miliyan uku da rabi ne ne.”
Za a ci gaba da binciken wadanda aka kama kan zargin har sai an gano bakin zaren, kamar yadda rundunar ’yan sandan ta sanar.