An kama jami’in Hukumar SEMA kan zargin sata

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) a Jihar Gombe sun kama Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, (SEMA) Dokta danlami Arab Rukuje bisa zargin karkatar da kayan agajin ’yan gudun hijira. Kayayyakin da ake zargin sun hada da bokitan fenti da buhunan siminti da Kwamitin PCNI ya bai wa […]

An kama jami’in Hukumar SEMA kan zargin sata

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) a Jihar Gombe sun kama Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, (SEMA) Dokta danlami Arab Rukuje bisa zargin karkatar da kayan agajin ’yan gudun hijira.

Kayayyakin da ake zargin sun hada da bokitan fenti da buhunan siminti da Kwamitin PCNI ya bai wa jihar, amma ba a kai wa sansanonin ’yan gudun hijirar ba.

Maimakon haka an karkatar da su zuwa wasu sassa da suka hada da kasuwanni inda aka sayar da su. Kuma sakamakon samun bayanan sirri da bincike ne aka gano shagunan da aka sayar da kayayyakin.

Kuma an kai samame a Kamfanin Harhada Takin Zamani na Jihar Gombe, inda aka boye wasu kayayyakin. Kuma nan take aka kama wani mai kula da sashin ajiye kayayyaki na kamfanin mai suna Isa Garba.

Bayan tsananta bincike ne aka sake kama wani ma’aikacin kamfanin mai suna Mu’azu Suleiman KT. 

An saki wadanda ake zargin bisa beli amma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.