An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya

Dubun masu yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Zariya ta cika.

An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya

Wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifi (Daga taskarmu).

An kama kanin wani magidanci a cikin ’yan bindigar da suka yi garkuwa da matar wansa a yankin Dutsen Abba ta Karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna.

Wan nasa shi ne Kansilan Dutsen Abba, Abdulaziz Sani kuma ’yan sintiri sun damke shi ne tare da abokansa biyu bisa zargin yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri a yankin.

Da misalin karfe 11 na dare ’yan bindiga suka afka wa kauyen Unguwar Hazo da ke Dutsen Abba suka kashe wasu matasa biyu; Musa Isa mai shekara 28 da Yusuf Sulaiman mai shekara 30.

Maharan sun harbi wata tsohuwa mai shekar 64 da wata mai shekara 50, da yanzu suke kwance a asibiti ana jinyar su.

’Yan bindigar sun far wa kauyen Madaka a ranar Alhamis inda suka yi garkuwa da matar Kansila Abdulaziz mai suna Samira da wata matar aure.

Sun kuma yi kwace babura hudu kirar Boxer a gidan Kansilan.

Amma Kungiyar Sintiri ta Jihar Kaduna da ke Unguwar Mai Tirmi a Karamar Hukumar Igabi ta tare maharan tare da ceto matan da kuma baburan daga hannunsu.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya