An kama kansila da basarake kan satar tiransfoma a Gombe

An kama kansilan yankin Kumo ta Gabas tare da wani basarake kan zargin su da sace tiransfoma a Jihar Gombe

An kama kansila da basarake kan satar tiransfoma a Gombe

’Yan sandan sun kama Kansilan yankin Kumo ta Gabas a Jihar Gombe, Abdullahi M Panda, kan zargin sacewa tare da sayar da tiransfomar wutar lantarkin garin Majidadi da ke yankin.

An kama shi ne tare da jauron majidadi, Muhammad Majidadi, da wani mutum daya a yankin da ke Karamar hukumar Akko a Jihar ta Gombe.

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta gabatar da su biyun tare da wani ne  bayan an kama su.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, CP Hayatu Usman, ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce, bayan samun rahotannin sirri ne suka kama wadanda ake zargin.

Ya ce da aka gudanar da bincike aka gano cewa an sayar da tiransfomar ne ga wani mai suna Bello Ardo Kumo a kan kudi Naira miliyan daya da dubu dari biyar.

Buhari ya ce tuni aka dawo da tiransfomar ana kan bincike, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

Wakilinmu ya ji ta bakin hakimin kauyen, Muhamamd Majidadi, inda ya bayyana masa cewa taransfomar ta shafe shekaru goma a ajiye ba tare an hada ta ba, har bata-gari sun sace wasu kayan cikinta.

Majidadi ya ce kafin su yanke shawarar sayar da tiransfomar sai da suka tara al’ummar garin suka nemi shawararsu kuma suka amince a sayar da ita a gina makarantar Islamiyya da Rijiya a garin.

A cewarsa, sai da ya yi magana da hakiminsa, shi kuma ya tuntubi kansilansu.

A nasa bangaren kansilan yankin Kumo ta gabas Abdullahi M Panda, ya ce ya yi magana da hakimin kauyen nasu kan batun tiransfomar, amma ya bukaci su kawo a  rubuce.

Daga nan ya sami hakimin wanda ya ce su jira zuwa ranar Litinin, kafin nan suka yi gaggawar kiran mai saye ranar Juma’a, shi kuma yana kokarin daukar Tiransfomar ne ’yan sanda suka kama su.

Abdullahi ya ki amsa laifin sa sai dai ya bukaci ’yan sanda da su kai su kotu inda zai shaida wa kotu abin da ya sani dan kubutar da kansa daga wannan zargi.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda