An kama karuwai dubu uku a Abuja

Kwamitin Musamman kan Tsabtace Birnin Abuja da Kula da shi ya kama kimanin karuwai dubu uku a cikin kwana casa’in a Abuja. Wata sanarwa da ta fito daga mataimakin darakta kuma babban sakataren labarai na Hukumar Birnin Tarayya Muhammd Sule ce ta bayyana haka, inda ta ce, Babban Sakataren Hukumar Birnin Mista John Chukwu ne […]

An kama karuwai dubu uku a Abuja
An kama karuwai dubu uku a Abuja

Kwamitin Musamman kan Tsabtace Birnin Abuja da Kula da shi ya kama kimanin karuwai dubu uku a cikin kwana casa’in a Abuja.

Wata sanarwa da ta fito daga mataimakin darakta kuma babban sakataren labarai na Hukumar Birnin Tarayya Muhammd Sule ce ta bayyana haka, inda ta ce, Babban Sakataren Hukumar Birnin Mista John Chukwu ne ya bayyana haka ga Kwamishinan ’Yan sandan Birnin Tarayya, Mista Wilson Inalegwu lokacin da ya ziyarce shi a Abuja.
Mista Chukwu ya ce, “Baya ga haka, an rufe haramtattun wuraren dibar yashi da na fasa duwatsu guda takwas da dakunan kwana na katako guda 205 da haramtattun kasuwannin 89 da wuraren sayar da motoci guda bakwai da shagunan sayar da abinci da na sana’ar kafinta guda 98 da suke a wuraren da aka haramta a cikin birnin.”
Babban Sakataren ya kara da cewa hukumar birnin ta kama masu talla da barace-barace a kan titi su dubu biyu da 534, sai kuma dabbobin da ke karakaina 102 da aka kama a haramtacciyar kasuwar dabbobi ta Gududa sauran sassan birnin a wannan lokaci da ake magana.