An kama kayan fasa kwauri na miliyan N80 a Kano

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa shiyyar Jihohin Kano da Jigawa ta kama mutum 15 bisa zargin fasa-kwaurin kaya da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 80. Kayan, wadanda suka hada da tireloli guda hudu dauke da buhunan gurbataccen takin zamani 1,842, buhunan shinkafa 1,608, jarkokin mai 567, buhuna 113 na suga, kulli 278 na […]

An kama kayan fasa kwauri na miliyan N80 a Kano

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa shiyyar Jihohin Kano da Jigawa ta kama mutum 15 bisa zargin fasa-kwaurin kaya da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 80.

Kayan, wadanda suka hada da tireloli guda hudu dauke da buhunan gurbataccen takin zamani 1,842, buhunan shinkafa 1,608, jarkokin mai 567, buhuna 113 na suga, kulli 278 na tabar wiwi, sai kuma diloli 20 na kayan gwanjo da kekunan hawa guda 20.

Da yake bajekolin kayayyakin a ranar Talata a Kano, Kwanturolan hukumar a shiyyar, Ahmad Nasiru ya ce tuni aka bayar da belin wadanda ake zargin yayin da bincike ke ci gaba da wakana.

Kwanturolan ya ce sun kwace kayan ne cikin watanni biyun da su gabata, yana mai bayyana masu fasa kwauri a matsayin masu yin zagon kasa ga ci gaban tattalin arzikin kasa.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba hukumar tasu hadin kai wajen ganin an kakkabe masu fasa kwaurin

“Ina kira ga jama’a da su ci gaba da ba mu muhimman bayanai cikin sirri da za su taimaka wajen ganin an kawo karshen ayyukan masu fasa kwauri,” inji kwaturolan.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya