An kama kifi mai nauyin kilo 145 a Kanada
Wasu masunta a kasar Kanada sun kama kifi mafi nauyi da girma a duniya a kasar Kanada. Shi dai wannan kifi da aka kama, yana da nauyin kimanin kilo 145, sannan kuma yana da tsayin kafa 9. Wasu masunta ne su biyu suka kama wannan kifi a lokacin da suke kama kifi a rafin Matane, […]
Wasu masunta a kasar Kanada sun kama kifi mafi nauyi da girma a duniya a kasar Kanada.
Shi dai wannan kifi da aka kama, yana da nauyin kimanin kilo 145, sannan kuma yana da tsayin kafa 9.
Wasu masunta ne su biyu suka kama wannan kifi a lokacin da suke kama kifi a rafin Matane, wanda wannan kifi ne ya zamo mafi girma da aka taba kamawa a tarihin kamun kifi.
Masunta masu suna Rene Kirouac da Raymon Bergeron, sun ce suna cikin sana’arsu ne sai suka lura da wani irin tafiya mai jirkita ruwa mai daure kai a cikin ruwan a kusa da wani dutse. Da suka je kusa da wajen sai suka ga ashe wani babban kifi ne da ba su taba ganin kamarsa ba, wanda hakan ya sa suka yi damarar kama shi.
Koda suka lura cewa ba za su iya kama kifin ba da fatsin da suke amfani da shi, sai suka yi maza suka je suka dauko bindigar farauta.
“Wannan ne kifi da muka kama mafi wahala a rayuwata, inji Mista Kirouac, wanda ya kasance tsohon masunci ne.
“Abin ban mamaki shi ne yadda kifin ya ki mutuwa duk da bugu da harbin da muka masa. Mun harbe shi a kusa da kusa, kuma muka ta yin harbin, amma ya ki mutuwa, sannan muka yi amfani da karfe mai nauyi muka ta buga masa a kai, shi ma bai yi amfanin komai ba. Amma dai daga baya da kyar muka samu nasarar kama shi.”
Bayan an samu labarin kifin, sai aka tura masa daga jami’ar kuebec da Rimouski (UkAR) karkashin Farfesa Denis Langebin domin su duba tare da bayyana irin halittar.
Hakanan kuma masu kididdiga da ajiye tarihi na Guinness Book of records sun tabbatar da cewa wannn kifi shi ne kifi mafi girma da tsawo da nauyi a duniya. Sannan aka dauki hoton kifin aka ajiye a matsayin tarihi.