An kama korarren soja da ke wa ’yan bindiga safarar makamai

Sojoji sun cafke wani kokararren soja da ke yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Jihar Filato da ke yawan fama da hare-hare.

An kama korarren soja da ke wa ’yan bindiga safarar makamai

Sojojin Najeriya

Sojoji sun cafke wani kokararren soja da ke yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Jihar Filato da ke yawan fama da hare-hare.

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce sojoji daga rundunar Operation Safe Haven sun kwace miyagun makamai ciki har da bindiga kirar AK-47 a hannun korarren sojan da dubunsa ta cika.

Daraktan ayyuka na hedikwatar tsaron, Manjo-Janar Edward Buba ya ce dubun korarren sojan ta cika ne a samamen da sojoji suka yi a kananan hukumomin Mangu da Barkin Ladi na Jihar Filato inda suka lalata maboyar ’yan bindiga.

Manjo-Janar Edward Buba ya ce a yankin Mangu, sojoji sun samu ’yan bindiga sun kai hari a kauye Kombili, amma maharan suka tsere bayan sun hangi sojojin, wadanda daga baya suka yi wa kauyen kawanya don cafke maharan, inda suak gano bindigar da maharan suka jefar.

Edward Buba ya ce a yankunan Kajuru da Jema’a na Jihar Kaduna kuma “Sojoji sun cafke miyagu da yawan gaske, ciki har da wani mai garkuwa da mutane, suka kuma kwato makamai masu tarin yawa.”

Ya kara da cewa sojojin sun kuma gudanar da irin wannan aikin a yankin Katsina-Ala na Jihar Binuwai, wadda ita ma take makwabtaka da Filato.

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa