An kama kurtun soja kan zargin satar alburusai a Borno

Sojan ya mallaki alburusai 756 na musamman da tulin gurneti da aka ɓoye a cikin wani ƙaramin buhun shinkafa.

An kama kurtun soja kan zargin satar alburusai a Borno

Dakarun Operation Haɗin Kai na Rundunar Sojin Ƙasa da ke Maiduguri a Jihar Borno, sun kama wani kurtun soja mai suna Lance Corporal Mubarak Yakubu bisa zargin satar alburusai.

A rahoton da aka tattaro na cewa rundunar ‘yan sandan Soja ta 7 da ke Dibishin mai lamba ta K9 ce ta kama sojan a yayin aikin bincike na yau da kullum da take yi a tashar mota ta Borno Express da ke Maiduguri a ranar 9 ga Mayu, 2024.

Majiyar leken asiri ta shaida wa ƙwararren masani kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, cewa sojan ya mallaki alburusai 756 na musamman da tulin gurneti da aka ɓoye a cikin wani ƙaramin buhun shinkafa.

Yanzu haka dai sojan yana hannun rundunar domin ci gaba da bincike a kansa.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja