‘Kwamandan Hisba da basarake sun sayar da jariri a Kano’

Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) ta kama wani Kwamandan Hisba da Mai Unguwar Fage a Jihar Kano, bisa zargin sayar da jariri dan shekara daya a Jihar Imo. Shugaban NAPTIP na yankin Kano, Shehu Umar a hirarsa da ‘yan jarida, inda ya ce wadanda ake zargin sun sayar da jaririn da wadda ta siyaye shi […]

‘Kwamandan Hisba da basarake sun sayar da jariri a Kano’

Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) ta kama wani Kwamandan Hisba da Mai Unguwar Fage a Jihar Kano, bisa zargin sayar da jariri dan shekara daya a Jihar Imo.

Shugaban NAPTIP na yankin Kano, Shehu Umar a hirarsa da ‘yan jarida, inda ya ce wadanda ake zargin sun sayar da jaririn da wadda ta siyaye shi sun amsa tambayoyin hukumar.

Wata majiya ta ce an bai wa jami’an Hisban alhakin kula da jaririn ne sakamakon jefar da shi da iyayensa suka kayi a kano.

An ce Kwamandan na Hisba ya yi amfani da damar da hadin kan Mai unguwar suka sayar da jaririn.

Shugaban na NAPTIP ya ce an kwato yaron da ake zargin masu laifin sun sayar ne daga wajen mahaifiyar matar wadda suka kamo daga Jihar Imo.

“Bayan samun rahoto kan lamarin, mun gudanar da binciken da ya taimaka muka kamo mahaifiyar Loveth a Jihar Imo,” inji Umar.

Ya ce an bayar da belin wadanda ake zargin amma akwai yiwuwar su kwashe shekara biyar a gidan kaso ko tarar naira miliyan biyar in har zargin ya tabbata.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato