An kama kwamandan Hisbah da matar aure a dakin otel a Kano
An ritsa jami’in da ya fi fice wurin kame karuwai tare da matar aure a unguwar Sabon Gari
Jami’an tsaro su cafke wani babban jami’in Hisbah tare da wata matar aure a wani dakin otal a unguwar Sabon Gari da ke Jihar Kano.
Jami’in Hisban da Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kano ta kama da matar auren shi ne ke jagorantar bangaren kamen matan da ke yawon banza na Hukumar.
- Magidanci ya kama matarsa tana soyayya da tsohon mijinta
- Yadda ‘dattawa’ ke goya wa matasa baya suna ta’asa a Jos
- Abubuwan da suka jawo tsadar abinci a lokacin kaka
- Uwargida ta kona mijinta da amaryarsa
’Yan sanda sun tsare shi ne bayan da suka dana masa tarko sakamakon korafi da mijin matar ya yi musu a kansa.
Aminiya ta gano cewa ritsa babban jami’in na Hisbah ne tare da matar auren ne a cikin wani dakin otal din da ke unguwar Sabon Gari ne a birnin Kano.
Da ’yan sanda suke masa tambayoyi, ya bayyana musu cewa ’ya take a wurinsa, rikici ne tsakaninta da mijinta shi ya sa ya kama mata dakin otel zuwa lokacin da za a warware matsalar.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina, ya shaida wa Aminiya cewa, “Mun kafa kwamiti mai mutum biyar don gudanar da cikakken bincike game da batunMun riga mun kafa kwamiti mai mutum biyar kuma mun ba su wa’adin kwana uku don bincikar lamarin.
“Za kuma mu nemi dukkanin bangarorin da al’amarin ya shafa don jin bayanansu,” kamar yadda ya bayyana a safiyar Laraba.
Ibn Sina ya ce da zarar an same shi da laifi hukumar za ta hukunta shi daidai da laifin da ya aikata.
“Hukumar Hisbah tana da dokokinta don haka idan mun same shi da laifi za mu hukunta shi cikin huruminmu domin shi hukunci hurumi-hurumi ne.”