An kama kwamandojin Boko Haram 7 a Katsina bayan sun dawo aikin Hajji

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hukumar tsaro ta DSS ta tsare shugabannin ’yan ta’addan da dubunsu ta cika a filin jirgin sama na Katsina bayan dawowarsu daga aiki Hajji

An kama kwamandojin Boko Haram 7 a Katsina bayan sun dawo aikin Hajji

Taswirar Jihar Katsina

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kama wasu shugabannin kungiyar Boko Haram da ISWAP guda bakwai a filin jirgin sama na Katsina bayan dawowarsu daga aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa an mika shugabannin ’yan ta’addan da dubunsu ta cika bayan dawowa daga Kasa Mai Tsarki ga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS).

“Ina farin cikin sanar da ku cewa a makon da ya gabata, ranar Alhamis, an kama shugabannin Boko Haram da ISWAP bakwai a filin jirgin Katsina lokacin da suke dawowa daga aikin Hajji, kuma an mika su ga Hukumar DSS,” in ji Ministan.

A cewarsa, tsarin tantance shaidar ɗan ƙasa na zamani ya taimaka wajen gano shugabannin ’yan ta’addan, abin da ya bayyana a matsayin shaidar ingancin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa a fannin tantance shaidar ɗan ƙasa da tsaron iyakoki.

Tunji-Ojo ya yi wannan bayani ne a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Hukumar Tantance Shaidar Ɗan Ƙasa ta 2026 (NIMC Act).

Ya bayyana dokar a matsayin babbar nasara da za ta ƙara inganta tsaron cikin gida da kuma sauƙaƙa wa ’yan ƙasa samun damar yin mu’amala da gwamnati.

Kaman ’yan ta’adda ta zo ne bayan ikirarin Dakta Bashir Kurfi a wani shirin Trust TV, ya yi zargin cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin wasu ’yan bindiga zuwa aikin Hajji. Sai dai gwamnatin jihar ta musanta wannan zargi.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Ƙasa na Jihar Katsina, Nasir Mua’zu, ya fitar ta ce “Zargin ba shi da tushe, ba shi da hujja kuma ba shi da wata sahihiyar shaida.

”An ƙirƙiro shi ne don yaudara da karkatar da hankalin jama’a daga nasarorin da gwamnati da hukumomin tsaro ke samu wajen yaki da matsalar tsaro a jihar.”

Sanarwar ta nuna damuwa kan irin waɗannan zarge-zarge da ta ce ake yaɗawa a lokacin da hukumomin tsaro tare da goyon bayan gwamnati ke samun nasarori a yaki da ’yan bindiga da sauran miyagu.

Ta kuma zargi wasu mutane da ƙungiyoyi da siyasantar da sha’anin tsaro don amfanin kansu, tana mai cewa mutanen ba su ji daɗin yadda gwamnati ta ƙi mara baya ga shirye-shiryen da za su karkatar da kuɗaɗen jama’a daga ayyukan ci gaba ba.