An kama kwamishinan Ganduje bisa badaƙalar Naira biliyan guda
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta kama kwamishinan ayyuka na zamanin Gwamna Ganduje bisa zargin badaƙalar Naira biliyan guda. Rahotanni sun ce hukumar ta kama Injiniya Idris Wada Saleh bisa tuhumar biyan kuɗin ga kamfanonin North Stone Construction Company Nigeria Limited, Arfat Multiresources Limited da 1st Step Construction ba bisa […]
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta kama kwamishinan ayyuka na zamanin Gwamna Ganduje bisa zargin badaƙalar Naira biliyan guda.
Rahotanni sun ce hukumar ta kama Injiniya Idris Wada Saleh bisa tuhumar biyan kuɗin ga kamfanonin North Stone Construction Company Nigeria Limited, Arfat Multiresources Limited da 1st Step Construction ba bisa ƙa’ida ba.
Majiyarmu ta ce an yi gaggawar sakin kuɗin a watan Afrilun bana bayan da jam’iyyar APC ta faɗi a zaɓen gwamna.
Bidiyon Dala: Muhuyi zai binciki Ganduje
Abba Kabir ya dakatar da ma’aikatan da Ganduje ya ɗauka
Kuma an fitar da kuɗin da sunan kwangilar gyaran tituna sai dai binciken hukumar ya nuna ko ƙasa ba a yayyafa musu ba.
Kawo yanzu dai hukumar ta fara karɓar shaida daga ma’aikatan gwamnati bisa yadda aka basu umarnin sakin kuɗin cikin gaggawa.