An kama kwandasta ya saci Kwamfuta

’Yan sanda a Kaduna sun gurfanar da wani kwandasta mai shekaru 23 a gaban wata kotun majistare bisa zargin sa da haurawa gidan wani mutum ya saci waya da kwamfutar Laptop. Ana zargin matashin, dan unguwar Kurmin Mashi da ke jihar da aikata fashi da makirci, hadi da sata amma dai ya musanta zargin. Buhari […]

An kama kwandasta ya saci Kwamfuta

’Yan sanda a Kaduna sun gurfanar da wani kwandasta mai shekaru 23 a gaban wata kotun majistare bisa zargin sa da haurawa gidan wani mutum ya saci waya da kwamfutar Laptop.

Ana zargin matashin, dan unguwar Kurmin Mashi da ke jihar da aikata fashi da makirci, hadi da sata amma dai ya musanta zargin.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Chidi Leo, ya sanar da kotun cewa kwandastan ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Yuli a Kurmin Mashi, in da shi da wani abokinsa suka balle gidan wani mai suna Abubakar Shehu, suka shiga ta taga suka saci kwamfuta da wayar hannu da kudinsu ya kai Naira 240,000.

Ya ci gaba da cewa, “Makwabta ne suka ankara inda suka kama shi, sai dai abokin satar tasa ya cika wandonsa da iska”.

Laifin da ake zargin mutumin da shi ya saba wa sashi na 287, da 243 na kundin Final Kod din Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya bada belin wanda ake zargin kan Naira dudu dari, da sharadin gabatar da wanda zai tsaya masa da ya mallaki kwatankwacin kudin, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Agusta.