An kama kyanwa mai fasakwaurin kwayoyi zuwa gidan yari
‘Yan sanda na binciken yadda aka yi amfani da kyanwa wajen fsakwaurin miyagun kwayoyi da layukan wayar salula ga fursunoni a gidan yari a kasar Sri Lanka. Jami’an gidan yarin Walikada mai cike da matakan tsaro, da ke Colombo, babban birnin kasar ne suka gano kyanwar wadda aka daura wa kunshin sinadarin kwayar heroin mai […]
‘Yan sanda na binciken yadda aka yi amfani da kyanwa wajen fsakwaurin miyagun kwayoyi da layukan wayar salula ga fursunoni a gidan yari a kasar Sri Lanka.
Jami’an gidan yarin Walikada mai cike da matakan tsaro, da ke Colombo, babban birnin kasar ne suka gano kyanwar wadda aka daura wa kunshin sinadarin kwayar heroin mai nauyin gram 1.8.
Kyanwar na kuma dauke da layukan wayar salula guda biyu da katin memori card daure a jikinta, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta.
Ta cewa jami’an gidan yarin sun gano kyanwar ne a ranar Asabar 1 ga watan na Agusta.
‘Yan sandan kasar sun ce da fari sun tsare ta a wani daki domin gudanar da bincike amma ta tsere daga inda ake tsare da ita.
Sai dai sun ce hakan ba zai dakatar da binciken da suke yi ba, domin gano ko a baya an yi amfani da dabbar wajen shigar da sauran haramtattun kayayyaki gidan yarin.