An kama lauya kan bautar da karamar yarinya
An gurfanar da wani lauya bisa zargin safara da cin zarafi da bautar da wata yarinya mai shekara 11 a Jihar Legas. Haka nan, ana tuhumar lauyan da lakada wa yarinyar duka da waya tare da ji mata rauni a ido da kuma a sassan jikinta wanda hakan ka iya makantar da ita. Sojoji sun kashe […]
An gurfanar da wani lauya bisa zargin safara da cin zarafi da bautar da wata yarinya mai shekara 11 a Jihar Legas.
Haka nan, ana tuhumar lauyan da lakada wa yarinyar duka da waya tare da ji mata rauni a ido da kuma a sassan jikinta wanda hakan ka iya makantar da ita.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 6 a kasuwar ’yan ta’adda
- A gaggauta hukunta wadanda suka kashe Goni Aisami —NSCIA
An gurfanar da lauyan ne a Kotun Majastare mai zamanta a yankin Yaba, karkashin jagorancin Alkali P.E Nwaka.
Bayanan kotun sun nuna lauyan da lamarin ya shafa ya dauki yarinyar ne don ta zame masa tamkar baiwa.
Sauran laifukan da ake zargin lauyan da su, har da hadin baki wajen safarar yarinyar, ji mata rauni da sauransu.
Mai gabatar da kara, Olofin Williams ya fada wa kotu cewa laifukan sun saba Sassa na 411, 276(a), 172, 173, 246 da kuma sashe na 245 na Kundin Dokokin Jihar Legas na 2015.
Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake yi masa.
Daga nan Alkali Nwaka ya ba da belin wanda ake zargin kan kudi N200,000 da mutum biyu masu tsaya mishi, tare da ba da umarnin damka yarinyar ga ofishin kula da walwala na jihar.
An dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Satumba, 2022.