An kama lauyan bogi yana tsaka da aiki a kotu

Wani lauyan bogi ya shiga hannu a lokacin da ya halarci zaman kotu domin kare wasu mutane da suka dauke shi aiki. ‘Yan sanda sun damke shi ne ana tsaka da zaman Babbar Kotun Tarayya da ke Abeokuta, Jihar Ogun inda yake kare wasu mutum biyar. Rahotanni sun nuna mutumin ya dade yana aikin lauya […]

An kama lauyan bogi yana tsaka da aiki a kotu

Wani lauyan bogi ya shiga hannu a lokacin da ya halarci zaman kotu domin kare wasu mutane da suka dauke shi aiki.

‘Yan sanda sun damke shi ne ana tsaka da zaman Babbar Kotun Tarayya da ke Abeokuta, Jihar Ogun inda yake kare wasu mutum biyar.

Rahotanni sun nuna mutumin ya dade yana aikin lauya a kotunan da ke jihar Ogun, kananansu da manyansu kafin dubunsa ta cika.

Tambayar da wani lauya ya jefa masa a lokacin da ake tsaka da sauraron shari’a ta jefa shakku a game da kasancewar sa lauya.

Alkalin kotun ta tambaye shi matakin da ya kai na karatu amma ya ce bai kammala makarantar koyan aikin lauya (Nigerian Law School) ba.

Ya ce ta fadi jarabar a kammala makarantar, don haka ba a tabbatar masa da zama lauya ba.

Da jin haka sai alkalin kotun mai Shari’a Kunle Somorin ya sa ‘yan sanda su tsare lauyan bogin.

‘Yan sanda sun tafi da mutumin caji ofis domin yi masa tambayoyi kafin gurfanar da shi a kotu a ranar 12 ga watan Agusta.

An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Legas

Hajjin 2025: An sanar da kamfanonin da za su yi jigilar maniyyata

Boko Haram sun kashe manoma 40, wasu sun ɓace a Borno

Yadda muka kashe manyan yaran Bello Turji —Sojoji