An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina
Daga cikin majinyatan nasa har da ƙasurmin da ake nema Usman Modi Modi, wanda aka sanar da bada ladar Naira miliyan 50 don nemo shi.
![An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/Doctor.png)
Jami’an tsaro sun kama wani ma’aikacin lafiya da ake zargi da yi wa wasu ’yan bindiga da suka raunata magani a Ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Daga cikin majinyatan nasa har da ƙasurmin da ake nema Usman Modi Modi, wanda aka sanar da bada ladar Naira miliyan 50 don nemo shi.
A cikin wani bidiyo da wani mai sharhi kan harkokin tsaro Zagazola Makama ya samu, wanda ake zargin mai suna Lawan Ado, ya amsa laifin jinyar wasu ’yan bindiga da suka jikkata.
A cikin bidiyon, ya ce ’yan bindigar za su ɗauke shi su kai shi maɓoyarsu a duk lokacin da suke buƙatar magani don neman lafiya.
A cewarsa, ɗan bindigan da ya fara yi wa magani shi ne Usman Modi Modi bayan da shugaban ƙungiyar su ya samu raunuka a wata arangama da ƙungiyar ’yan banga ta Yan Kyanbara.
“Da farko an kai shi wani asibiti a Taskiya domin yi masa magani, amma bayan kwana biyu, sai suka kawo ni don in ƙara yi masa magani. An biya ni Naira 18,000 don kula da lafiyar waɗanda aka raunata,” cewar likitan da ake zargin.
Ado ya ƙara da cewa yana jinyar wasu manyan ’yan bindiga da suka haɗa da Mai Kudi wanda ya biya shi Naira 8,000 bayan an harbe shi a Kurfi.
Ya ce, haka ma ya yi wa Audu, mai taimaka wa Usman Modi Modi, wanda shi ma ya biya Naira 8,000.
Ya ƙara da cewa, “Dogo Mardi, wanda ya samu raunin harbin bindiga a yayin wani harin fashi da makami ya biya ni N11,000”.
Ya bayyana cewa ya yi tafiya zuwa wasu wurare domin jinyar ’yan fashi, ciki har da wanda aka bayyana da Karanboguwa.