An kama likita kan laifin yin tsafi da sassan jikin mutum
Wani likita mai suna Dokta Babawale Funsho Joshua, ya shiga hannun ’yan sanda bisa tuhumar yanke sassan jikin gawar wani yaro a jihar Ogun.Babawale, wanda aka kama tare da wasu abokan huldarsa su uku, shi ke da asibitin Ajike Medical Centre da ke Sango Otta a Jihar Ogun.Jami’in hulda da jama’a na hukumar ’yan sanda […]
Wani likita mai suna Dokta Babawale Funsho Joshua, ya shiga hannun ’yan sanda bisa tuhumar yanke sassan jikin gawar wani yaro a jihar Ogun.
Babawale, wanda aka kama tare da wasu abokan huldarsa su uku, shi ke da asibitin Ajike Medical Centre da ke Sango Otta a Jihar Ogun.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ’yan sanda na jihar, Muyiwa Adejobi ya ce an kama shi ne bisa tuhumar hada kai da wasu wajen yanke sassan jikin wani yaro dan wata 13 da ya mutu a asibitinsa ranar takwas ga Yunin bana.
Tuni aka kai gawar jaririn zuwa mutuwaren babban asibitin Ifo, don gudanar da binciken musababbin mutuwarsa. Sauran mutum uku da aka kama su tare da likitan sun hada da Oguntunde Opeyemi da Olaide Adeyanju da Temitope Muraina.