An kama ‘likita’ ya yi basaja da hannun roba don guje wa rigakafin COVID-19
’Yan sanda sun cafke jami’in lafiyar bisa zargin yaudara domin kar a yi masa allurar rigakafin COVID-19
An kama wani ma’aikacin lafiya a kasar Italiya bayan je karbar allurar rigakafin COVID-19 a hannun roba don kar allurar ta shiga jikinsa.
Ma’aikacin lafiyan ya nade damtsen hannunsa ne da roba saboda kar allurar da za a yi masa ta shiga jikinsa.
- Gwarzon Dan Kwallon Duniya: Yadda nasarar Messi ta jawo muhawara
- Ba mu da hannu a kone ofishin Sanata Barau —APC
Bayan zuwa asibitin domin karbar allurar ce nas din da za ta yi wa mutumin mai shekaru 50 allurar ta gano dabarar tasa.
Da ya ga haka sai ya roke ta cewa ta rufa masa asiri amma ta ce allambaram, ta sanar da ’yan sanda, da zarginsa da yaudara.
Nas din ta sanar da kafafen yada labarai cewa bayan ta nade hannun rigarsa za ta yi masa allurar ce ta lura damtsensa ba kamar na dan Adam ba, babu dumi kuma ya yi kamar roba.
Mutumin da ya yi hakan jami’in lafiya ne da aka dakatar daga zuwa aiki saboda ba a yi masa allurar rigakafin COVID-19.
A kasar Italiya dai an wajabta wa ma’aikatan lafiya yin allurar rigakafin COVID-19.
Yanzu dai ’yan sanda a yankin Biella, da ke Arewa Maso Yammacin Italiya na bincike kan lamarin.