An kama likita yana rubuta wa matarsa jarrabawa
Rundunar tsaro ta farin kaya da ake kira sibil difens ta kama wani likita da ke aiki a Babban Asibitin Gumel a Jihar Jigawa bisa zarginsa da kokarin yin magudin jarrabawa ta hanyar rubuta wa matarsa jarrabawar nema shiga jami’a (JAMB) da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.Likitan mai suna Ifeanyi Eze wani […]
Rundunar tsaro ta farin kaya da ake kira sibil difens ta kama wani likita da ke aiki a Babban Asibitin Gumel a Jihar Jigawa bisa zarginsa da kokarin yin magudin jarrabawa ta hanyar rubuta wa matarsa jarrabawar nema shiga jami’a (JAMB) da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
Likitan mai suna Ifeanyi Eze wani dan kabilar Ibo da ke aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar jami’an tsaron farin kayan sun kama shi ne yana rubuta wa matarsa mai suna Ifeoma Eze
Callissta wadda ita ma ’yar kabilar Ibo ce daga Jihar Ebonyi jarrabawa.
An kama likitan ne a cibiyar zana jarrabawa ta makarantar Kimiyya da kere-kere da ke Lautai a lokacin da yake cikin zana wa matar tasa jarrabawar.
An kama Efeanyi da takardar jarrabawar mai lamba P11704 ta cibiyar jarrabawa yayin da kuma takardar jarrabawar take dauke da lamba kamar haka: No 45452644 BC.
Tuni aka mika shi ga ’yan sanda domin ci gaba da yi masa tambayoyi kafin gurfanar da shi a gaban kotu.
Shugaban Hukumar tsaro ta farin kaya Alhaji Muhammed Gidado ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ya zama dole a sanya ido kan yadda wasu suke amfani da wata dama wajen aikata magudin jarrabawa.