An kama likitan bogi bayan ya shekara 10 yana aiki

  Rundunar ‘Yan Sanda da taimakon Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Hakori ta Kasar (MDCN) ta kama wani mutum wanda yake aiki a wani asibiti mai zaman kansa har tsawon shekara 10 a unguwar Gwarimpa da ke Abuja. Mutumin mai suna,Victor Moffat Akpan, shi ne wanda ya mallaki asibitin Luna Maternity & Surgery. An dai budee […]

An kama likitan bogi bayan ya shekara 10 yana aiki

 

Victor Moffat AkpanRundunar ‘Yan Sanda da taimakon Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Hakori ta Kasar (MDCN) ta kama wani mutum wanda yake aiki a wani asibiti mai zaman kansa har tsawon shekara 10 a unguwar Gwarimpa da ke Abuja.

Mutumin mai suna,Victor Moffat Akpan, shi ne wanda ya mallaki asibitin Luna Maternity & Surgery.

An dai budee asibitin ne a shekarar 2006, “inda yake amfani da takardun bogi.”

Har ila yau, an gano cewa mutumin da ake zargin shi ne ya jaroganci wani aikin raba wasu ‘yan tagwaye da aka haife su a manne, wadanda kuma suka rasu daga bisani a Babban Asibitin Abuja a shekarar 2013.

Jami’in Kungiyar MDCN Dokta Henry Okwuokenye ya ce sun gudanar da bincike a kan wanda ake zargin, amma kungiyarsu ba ta ba shi takardar amincewa ya fara gudanar da aiki ba, saboda makarantar da yake ikirarin cewa ya kammala ba ta da  amincewar hukuma.