An kama Likitan bogi wanda bai kammala karatun firamare ba

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama Abdulrahman Mohammed da ke daukar kansa a matsayin kwararren Likita. A binciken da rundunar ta yi game da Abdulrahman Mohammed ta gano ya shafe kimanin shekara hudu yana gudanar da aikin Likitanci ta hanyar bayar da magunguna da yin gwaje-gwajen jini da na fitsari da yi […]

An kama Likitan bogi wanda bai kammala karatun firamare ba

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama Abdulrahman Mohammed da ke daukar kansa a matsayin kwararren Likita. A binciken da rundunar ta yi game da Abdulrahman Mohammed ta gano ya shafe kimanin shekara hudu yana gudanar da aikin Likitanci ta hanyar bayar da magunguna da yin gwaje-gwajen jini da na fitsari da yi wa marasa lafiya allura da ba su magunguna ba bisa ka’ida ba.

A binciken an gano Mohammed bai kammala karatun firamare ba amma ya shiga harkar Likitanci a tsawon shekaru hudun da ya kwashe yana wannan sana’a ba tare da sanin kowa ba.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas Mista Imohimi Edgal ne ya sanar da manema labarai haka a lokacin da yake gabatar da Likitan bogin tare da kayayyakin aikin Likitancin a Mushin da ke Jihar Legas a karshen makon jiya.

Likitan bogin mai shekara 39 ya fito ne daga garin Ran na karamar Hukumar Gambaru Ngala da ke Maiduguri na Jihar Borno.

Wanda ake tuhumar yana da shagon da yake gudanar da aikin Likitancin ne a Lamba 3 da ke Layin Bamismiele da ke Idi-Araba da ke Legas kafin a yi ram da shi.

A binciken da aka yi a kan Mohammed, ya ce ya yi karatun firamare amma ya kasa gabatar da shaidar kammala karatun na firamare da hakan ta sa ake kokwanton bai ma yi karatun ba.

A lokacin da manema labarai suka zanta da shi, Likitan bogin ya nuna bai dauki kansa a matsayin kwararren Likita ba, yana dai taimaka wa jama’a ne wajen yin gwaje-gwajen jini da na fitsari da kuma sayar musu da magunguna ciki har da allurai.  Ya ce yana sayo magungunan ne daga kasuwar Idumota da ke Jihar Legas inda yake sayar wa jama’a. Ya ce tun a shekarar 2014 ce ya tsunduma a wannan harkar bayan ya koma Legas daga Jihar Borno saboda matsalar ’yan Boko Haram da ta yi katutu a Maiduguri inda ya rungumi sana’ar Likitanci.