An kama limami saboda hudubar kada a zabi Gwamnan Yobe
Wasu da ake kyautata zaton jami’an tsaro ne sun yi awon gaba da Ustaz Abubakar Chiroma Limamin Masallacin Juma’a na rukunin gidajen kan hanyar Gujba da ke garin Damaturu fadar Jihar Yobe, bisa zarginsa da gabatar da wata huduba da aka ce ya kira yi jama’a a kan kada su zabi Gwamna mai ci a […]
Wasu da ake kyautata zaton jami’an tsaro ne sun yi awon gaba da Ustaz Abubakar Chiroma Limamin Masallacin Juma’a na rukunin gidajen kan hanyar Gujba da ke garin Damaturu fadar Jihar Yobe, bisa zarginsa da gabatar da wata huduba da aka ce ya kira yi jama’a a kan kada su zabi Gwamna mai ci a jajibaren zaben gwamnoni da ’yan majalisar jihohi da aka yi a ranar 11 ga Afrilun nan.
Aminiya ta samu labarin cewa Malam Abubakar a cikin hudubar wadda ta haifar masa da jangwam ya ce kowa yana da damar da zai zabi wanda yake so, inda aka ce ya zargi Gwamna mai ci da cewa babu wani abin a zo a gani da ya yi wa al’ummar jihar.
Bayan kammala zabe sakamako ya fito da ke nuna Gwamna Ibrahim Gaidam na Jam’iyyar APC ya lashe zaben a ranar Talata, sai wasu da ake zaton jami’an tsaro ne suka je gidan malamin suka tafi da shi kamar yadda wata majiya ta kusa da iyalansa ta shaida wa Aminiya.
Tun lokacin da jami’an tsaron suka tafi da malamin har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu labarinsa ballantana a san a ina yake ko a san su wa suka kama shi. Sai dai ana hasashen cewa kama malamin ba ya rasa nasaba da hudubar da ya yi.
Kakakin Gwamnan Jihar Abdullai Bego ya ce sam Gwamnan Jihar bai san wannan magana ba, balle ya sa a kama malamin. Ya ce sai dai a nemi jami’an tsaro na soja ko ’yan sanda don neman karin bayani kan dalilin kama malamin, amma dai gwamnatin Yobe ba ta da hannu wajen kama shi.
Aminiya ta tattauna da shugaban kungiyar Rundunar Adalci a Jihar Yobe, Malam Zakari Adamu dangane wannan lamari, inda ya ce babban rashin adalci ne don liman ya ce mutane su zabi wanda suke so gwamnati ta sa a kama shi. Ya ce, kungiyarsu ba za ta nade hannu kan wannan rashin adalci da kama karya ba, kuma yanzu suna shiryawa don zuwa kotu da nufin kwato wa malamin hakkinsa.