An kama limamin coci da mutum 6 bisa zargin tsafi da sassan mutum

’Yan sanda a Kurosriba sun kama wani babban limamin cocin   Royal God’s Commandment Ministry da ke lamba 3, layin Okon Edak, unguwar Atamunu, karamar Hukumar Kalaba ta kudu ta Jihar Kurosriba mai suna   Rabaran Tony Obo, tare da wasu mukarrabansa shida; sakamakon zarginsu da yin tsafi da sassan jikin dan Adam a majami’arsa. […]

An kama limamin coci da mutum 6 bisa zargin tsafi da sassan mutum

’Yan sanda a Kurosriba sun kama wani babban limamin cocin   Royal God’s Commandment Ministry da ke lamba 3, layin Okon Edak, unguwar Atamunu, karamar Hukumar Kalaba ta kudu ta Jihar Kurosriba mai suna   Rabaran Tony Obo, tare da wasu mukarrabansa shida; sakamakon zarginsu da yin tsafi da sassan jikin dan Adam a majami’arsa.

Lokacin da Aminiya ta ziyarci majami’ar a makon jiya, wakilinmu ya iske mutane da yawa sun taru suna kallon yadda wasu fusatattun matasa suka harzuka, suka rika rusa ginin majami’ar, wasu daga cikin kayayyakin majami’ar kuma suka kona su. Haka kuma sun rika zakulo kasusuwa da sauran sassan jikin dan Adam a baraguzan ginin dakunan cocin.

Ana cikin wannan hali ne wani mazaunin unguwar da ya zanta da wakilinmu bisa rokon a sakaya sunansa ya ce: “A na cikin wannan yanayi sai wasu daga cikin mutanen unguwar suka ga daya daga cikin wadanda Faston ya aiko suka sato wata karamar yarinya a unguwar ya zo wurin. Sai suka yi kukan kura, suka kama shi suka mika shi ga ’yan san sanda. Su kuma suka tafi da shi gidan Fasto, wanda yana ganinsu ya ce ya zai zo masa da wadannan mutane bayan sun yi jinga da su kuma ya biya su kudinsu.”

Irene Ugbo, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kurosriba, ta shaida wa Aminiya cewa limamin coci tare da wasu mutum shida na tsare a rundunarsu kuma suna bincikensu.