An kama limamin da ya daura wa gawa aure a Bauchi

An daura aure har da sadaki kafin a yi wa gawar jana’iza

An kama limamin da ya daura wa gawa aure a Bauchi

Kisa

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta kama wani limami da ya daura wa gawa aure a garin Bauchi.

Da yake tabbatar da labarin daura auren, wani ma’aikacin Hukumar, Malam Bahjatu Nasir ya ce hukumar ta kama limamin da ya daura auren da kuma ‘angon’ gawar.

‘Angon’ mai da ke Unguwar Kandahar a garin Bauchi ya ‘auri’ marigayiyar budurwarsa ce a ranar da ta mutu kan sadakin Naira dubu biyu.

Wata majiya ta ce, mamaciyar ce ta bukaci ko bayan ta rasu a daura musu aure da shi kuma a yi sadaka da kudin.

Mahaifiyar marigayiyar ce ta bayyana wasiyyar da ta bari jim kadan bayan rasuwkarta.

Wata ’yar uwar marigayiyar mai suna Hadiza ta ce watan uku da fara nema a tsakanin masoyan sai ta hadu da rashin lafiya, shi ne ta bar wasiyya cewa ko ta rasu ya bada sadakin Naira dubu biyu a daura musu aure.

Limamin da ya daura auren, ya ce yana limanci ne a Unguwar Nasarawar Dawaki kuma da suka samu labarin rasuwar budurwar suka je jana’iza ne uwar mamaciyar ta fito ta ce ta bar wasiyyar cewa ko ta rasu a yi musu aure da saurayin nata.

Ya ce ya tambayi ‘angon’, ya ce ya yarda da haka, shi ne suka yi addu’a suka daura mata aure.

‘Angon’ ya ce bayan budurwarsa ta rasu sun tambayi malamin da ya jagoranci jana’izarta ko hakan ya inganta a addini, inda ya ce eh tunda wasiyya aka bari wajibi ne a zartar da wasiyyar.

“To bayan nan kuma sai muka ji wadansu na cewa hakan bai inganta ba,” inji shi.

Ya ce ya gan ta ne aka ce bazawara ce, ya fara neman ta kuma sun yi wata uku suna nema, kuma bayan da aka yi ‘auren’ ya fada wa wakilinsa a fadada bincike a kai.

Ya ce ranar da aka yi ‘auren’ ba ya da kudi, ajalan aka daura, duk lokacin da ya samu zai biya a yi mata sadaka.

Ya ce a shirye yake idan malamai suka ce bai halatta ba, ya yi biyayya.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi