An kama mabaracin da ke samun Naira miliyan 10 da dubu 800 a wata a Dubai
Hukumar kula da birnin Dubai ta kama mabaracin da ke samun Dirhami dubu 270 a kowane wata, a cewar Faisal al Badawi, Shugaban sashen kula da kasuwanin birnin, a lokacin da yake karin haske game da kama mabarata 59 a watanni uku na farkon shekarar 2016.Kamen mabaratan wani shiri ne na hadin gwiwa tsakanin Hukumar […]
Hukumar kula da birnin Dubai ta kama mabaracin da ke samun Dirhami dubu 270 a kowane wata, a cewar Faisal al Badawi, Shugaban sashen kula da kasuwanin birnin, a lokacin da yake karin haske game da kama mabarata 59 a watanni uku na farkon shekarar 2016.
Kamen mabaratan wani shiri ne na hadin gwiwa tsakanin Hukumar birnin da jami’an ’yan sandan masarautar.
A cewar al Badawi, an gano cewa, a kalla wannan mabaraci yana samun kudin da suka kai Dirhami dubu tara a kowace rana, wato daidai da Naira dubu 36.
“Wasu daga cikin mabaratan suna da fasfo da ya yi nuni da cewa sun samu izinin shiga kasar don kasuwanci. A lokacin da ake fafutikar hana mabaratan yawo an gano cewa mafi yawan su sun shiga kasar ne bisa ka’ida, tare da bizar wata uku, ta yadda za su samu dammar dimbin kudi,” inji shi.
“Mun gano mabaracin da ke samun Dirhami dubu 270, wato a kalla Naira miliyan 10 da dubu 800. An dai fi samun kudi a ranar Juma’a, lokacin da mabaratan ke tsayawa a masallatai,” inji Al Badawi.
Hukumar birnin dai na ta ftafutikar hana bara a Dubai, musamman a wannan lokaci da azumin watan Ramadan ke karatowa. An kuma bai wa mazaunan birnin lambar wayar da za su sanar da jami’an tsaro da zarar sun ga mabarata.