An kama mabaraciya da Naira miliyan 13 a Makkah

Masu gabatar da kara suna bincike a kan mabaratan da suka hada da maza da mata

An kama mabaraciya da Naira miliyan 13 a Makkah

Wasu mabarata a Saudiyya

Jami’an tsaro a birnin Makka sun kama wata mabaraciya dauke da Riyal 117,000 (kusa Naira miliyan 13), baya ga kudaden kasashen waje da gwala-gwalai.

Kafar labarai ta Saudi Gazzett wadda ta ruwaito labarin a ranar Talatar da ta gabata, ta ce matar, ’yar asalin Asiya, tana cikin mabarata 3,719 da aka kama a sassan kasar a tsakanin ranakun 22 zuwa 30 ga Maris din bana.

Masu gabatar da kara suna bincike a kan mabaratan da suka hada da maza da mata.

Hukumomin Saudiyya dai sun hana barace-barace a kasar, inda suka nemi mutanen kasar su rika kai rahoton duk wanda suka samu yana bara ko yana ba mabaratan sadaka ta hanyar kiran layin tarho mai lamba 911 a yankunan Makka da Riyadh da kuma mai lamba 999 a sauran yankunan kasar.

Hukumomin tsaro sun ce kwararrun jami’an tsaro za su kama duk wanda aka gani yana bara tare da mika shi ga hukumomin da suka dace.

Kakakin Hukumar Tsaron Jama’a ta kasar Birgediya Janar Sami Al-Shwairekh ya ce za a hukunta duk wanda aka kama yana bara ko yana ingizawa a yi ko kuma yana taimakawa a yi barar.

Ya ce duk wanda aka samu da laifi za a daure shi a tsawon wata shida ko ya biya tarar Riyal dubu 50, (kimanin Naira miliyan 5, da dubu 543 da 130) ko a hada masa duka biyun.

Sannan za a ninka hukuncin ga duk wanda aka samu cikin kungiyoyin shirya barace-barace.