An kama mafarauta suna fashi a Adamawa
Wasu mafarauta sun shiga hannun bayan ’yan sanda sun cafke su bisa zargin aikata fashi da makami a Jihar Adamawa. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, Olugbenga Adeyanju, ya ce dubun mutanen wadanda ’yan Kungiyar Mafarauta ne ta cika ne bayan ’yan sanda a yankin Ganye sun yi arba da su. Za a rataye ’yan fashi […]
‘Yan sandan Najeriya suna farautar masu laifi a Birnin Gwari
Wasu mafarauta sun shiga hannun bayan ’yan sanda sun cafke su bisa zargin aikata fashi da makami a Jihar Adamawa.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, Olugbenga Adeyanju, ya ce dubun mutanen wadanda ’yan Kungiyar Mafarauta ne ta cika ne bayan ’yan sanda a yankin Ganye sun yi arba da su.
“Mun cafke mafarauta hudu da muka aminta da su domin su taya mu yakar manyan laifuka amma suka rikide suka koma fashi da makami kamar yadda daya daga cikinsu ya tabbatar mana.
“Hakan ya sa dole mu rika yin taka-tsantsan game da yadda za mu yi aiki samar da tsaro tare da mazauna al’ummomi”, inji shi.
Kwamishinan ya bayyana takaicin yadda wasu batagari ke kawo cikas yayin da gwamnatin jihar na jaddada muhimancin hada kai da al’ummomi wajen samar da tsaro.
Olugbenga Adeyanju ya yi jawabin ne a taron lalubo mafita domin magance rikicin makiyaya da manoma a jihar.
Da yake jawabi, Gwamna Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa amfani da makamai kadai ba zai magance matsalolin tsaro ba; dole an an tattauna tsakanin bangarori.
Shi ma a bangarensa, Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo ya bayyana damuwa game da yawaitar rikicin manoma da makiyaya.
Basaraken wanda Galadima Adamawa, Alhaji Mustafa Aminu ya wakilta ya ce magance matsalar na bukatar bin hanyoyi da dama da suka hada da shigar da sarakuna cikin harkokin tsaro da kuma samar wa jami’an tsaro kayan aiki na zamani.