An kama magidanci kan zargin yin luwadi da dan shekara hudu
Mutanen Unguwa sun kama wani magidanci da ake zargi da yi wa wani yaro dan shekara hudu fyade a a wani gidan kallon kwallo da ke Layin Lemu Tudun Wada, Zariya. Magidancin mai suna Bello wanda aka fi sani da Bello dankare mai kimanin shekara 38, kuma dan asalin Jihar Zamfara, a dalilin almajiranci […]

Mutanen Unguwa sun kama wani magidanci da ake zargi da yi wa wani yaro dan shekara hudu fyade a a wani gidan kallon kwallo da ke Layin Lemu Tudun Wada, Zariya.
Magidancin mai suna Bello wanda aka fi sani da Bello dankare mai kimanin shekara 38, kuma dan asalin Jihar Zamfara, a dalilin almajiranci ya je Zariya, inda ya shafe shekara 20 a unguwar.
’Yan sinitiri na unguwar sun shaida wa Aminiya cewa an sha kama wanda ake zargin kan irin wannan mugun aiki amma bayan ya gama zaman gidan kaso idan ya dawo sai ya ci gaba da aikata mugun aikinsa. Sun ce al’ummar unguwar sun sha alwashin ba za su sake bari ya zauna a unguwar ba inda suka yi kira kungiyoyin kare hakkin yara su shigo cikin lamarin domin ganin cewa an yi masa hukunci mai tsanani.
Wakilinmu ya zanta da malamin Bello dankare wanda aka sakaye sunansa, inda ya nuna damuwa kan yadda almajirin nasa yake aikata irin mugun hali. Ya ce bayan ya koma da shi garinsu ya yi aure har ya haihu amma ya gudo ya bar matar da dan a can. Ya ce yana goyon bayan matakin da jama’a suka dauka na raba shi da zama a unguwar koda ya dawo daga gidan kaso.
Babban Jami’in ’Yan sanda mai kula da ofishin Tudun Wada (DPO) ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni sun tura yaron da wanda ake zargin zuwa Babban Asibitin kofar Gayan domin gudanar da bincike, kuma da zarar sun samu sakamako za su tura shi babban ofishinsu da ke Kaduna don daukar matakin da ya dace.