An kama magidancin da ya yi garkuwa da kansa a Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum, da ya yi garkuwa da kansa don ya karbi kudi a hannun ’yan uwansa. Ado ya hada kai da matarsa da wani mutum ne, inda suka nemi ‘yan uwansa su biya kudin fansa Naira miliyan hudu. An yi garkuwa da uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna […]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum, da ya yi garkuwa da kansa don ya karbi kudi a hannun ’yan uwansa.
Ado ya hada kai da matarsa da wani mutum ne, inda suka nemi ‘yan uwansa su biya kudin fansa Naira miliyan hudu.
- An yi garkuwa da uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna
- ’Yan daba sun kashe mutum uku a zanga-zangar #EndSARS
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Abdullahi Haruna, ya ce asirinsu ya tonu ne sakamakon kama Alex da aka yi, sannan aka gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya kara da cewa sun kama wani mutum da ya yi wa wata karamar yarinya asiri ya aure ta a Jihar Gombe.
Haruna ya rundunar ta kama wasu mutum uku bisa zargin yin fyade ga wata karamar yarinya da kuma matar aure.