An kama mahaifi kan zargin sayar da ’ya’yansa saboda bashi
Ya yi niyyar sayar da ’ya’yan ne saboda tsananin talaucin da yake fama da shi.
Jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence a Jihar Akwa Ibom, sun cafke wani mutum yana kokarin sayar da ’ya’yansa biyu saboda kantar bashi da ta yi masa katutu.
Ana zargin mutumin da hada baki da matarsa wajen sayar da ’ya’yansu guda biyu biyu mata a kan Naira 700,000 domin ya biya bashi.
- Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin rataya kan kisan kawunsu
- Jirgin saman Najeriya zai soma jigila a Afrilun badi — Hadi Sirika
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Umana Ukeme ya fitar ranar Laraba, ta ce mutumin ya shiga hannu ne a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.
Umana Ukeme ya ce mutumin wanda ke ke rayuwa a Kasar Kamaru, ya shiga hannu ne tare da mai dakinsa a ranar 15 ga watan Nuwamba, bayan bincike sirri ya bankado yunkurinsa na sayar da yaran mata biyu.
Jami’in na hukumar NSCDC ya ce daya daga ’ya’yan mutumin akwai mai shekarun haihuwa shida sai kuma karamar mai shekaru hudu.
Sanarwar ta ambato mutumin mai shekara 40 da ake zargi yana cewa ya yi niyyar sayar da ’ya’yansu ne saboda tsananin talaucin da yake fama da shi.