An kama mahaifin da ya azabtar da dansa kan zargin maita

Wani magidanci mai kimanin shekara 34 ya shiga hannun jami’an Sibil Difens bisa zargin raunata dansa mai shekara 7 saboda zarginsa da maita. Mahaifin mai suna Daniel ya azabtar da dan nasa ne mai suna Desmond har ta kai ga ba ya iya tafiya sosai saboda duka. A cewar mahaifin, idan suna barci da dare […]

An kama mahaifin da ya azabtar da dansa kan zargin maita

Wani magidanci mai kimanin shekara 34 ya shiga hannun jami’an Sibil Difens bisa zargin raunata dansa mai shekara 7 saboda zarginsa da maita.

Mahaifin mai suna Daniel ya azabtar da dan nasa ne mai suna Desmond har ta kai ga ba ya iya tafiya sosai saboda duka.

A cewar mahaifin, idan suna barci da dare sai dan ya rika ihu shi kuma idan ya tambaye shi abin da ke sa shi ihun sai ya ce masa wai wata mata ce ke kiransa a cikin barci. “Wannan dabi’a ta ihu cikin dare ta sa nake zargin kamar ya shiga cikin kungiyar asiri ne ko kuma yana da maita, domin abin yana ba ni matukar takaici. Babban abin da ke damuna shi ne, kakarsa ta wajen uwa ta taba fada mini cewa ba zan sake aure ba a rayuwata tunda na ki auren ’yarta wato mahaifiyar Desmond bayan na yi mata ciki a lokacin muna soyayya.”

Ya ce, “Ni kuma wannan abin da ta fadi ya sa idan na ji yaron yana ihu cikin dare sai in dauka kamar ita kakar tasa ce matar da ke kiransa cikin dare. Shi ya sa na ji na tsane shi. Abu kadan sai in buge shi.”

Mahaifin ya bayyana wa Aminiya haka ne a gaban Kwamishinar Mata da Jin Dadin Marasa Galihu ta Jihar Kaduna, Hafsat Baba a lokacin da aka kawo yaron gabanta. 

Mahaifin ya ce uwarsa ta kawo masa yaron ne tun yana da shekara biyu da haihuwa saboda haka sai ya mika shi ga mahaifiyarsa ta taimaka ta raine shi. Ya ce “Na karbo shi ne daga wajen mahaifiyata bayan na yi aure a shekarar 2016. Shi kuma ya dawo wajena da zama a watan Dasumban 2017 domin in saka shi a makaranta amma dabi’unsa sun sa na ji yana ba ni haushi.”

Sai dai kuma ya nuna takaicinsa ganin halin da yaron ke ciki a sakamakon azabtar da shi na tsawon wata biyu da yaron ya yi a hannunsa. Da Aminiya ta tambaye shi inda mahaifiyar yaron take sai ya ce bai sani ba amma dai ya ji an ce ta yi aure.

Aminiya ta samu damar zantawa da yaron wanda ke fama da tsamin jiki domin fuskarsa a kumbure take sannan ga tabon duka a bayansa. Ya ce mahaifinsa ne ke dukansa. “Babana ke dukana kuma ni ban san abin da na yi ba. Amma ita Antina (matar mahaifinsa) ba ta duka na idan ta hana Baba sai ya ki daina dukana,” inji shi.

Kwamishina Hafsat Baba ta ba da umurnin a kai shi asibiti, inda ta kuma ce da wuya a mai da yaron wajen mahaifinsa domin gudun kada ya halaka shi. “Gaskiya abin takaici ne a ce mahaifi ya yi wa dannsa irin wannan mummunan duka saboda kawai zargin wani abu wai maita. Wannan ya nuna mahaifin ya yi imani da irin wadannan abubuwa ke nan. Saboda haka gwamnati za ta ci gaba da rike yaron domin ba za mu mika masa ba, domin kada ya je ya kashe shi. Shi kuma mahaifin na ba da umarnin a tsare shi kafin mu mika shi kotu domin hukunta shi,” inji ta.

Ta gargadi iyaye su guji azabatar da ’ya’yansu babu gaira babu dalili, domin a cewarta duk wanda aka kama ba zai ji da dadi ba.