An kama mahaifiyar Ronaldo da Naira miliyan 11 a filin jirgin saman Sifen

Jami’an tsaro sun cafke mahaifiyar Cristiano Ronaldo mai suna Dolores Abeiro da yunkurin barin kasar da Yuro dubu 45 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 11 da dubu 205 ba tare da an ba ta izinin yin hakan ba. Rahoton da kafar sadarwa ta The Telegraph ta kalato ya nuna, mahaifiyar dan kwallon mai […]

An kama mahaifiyar Ronaldo da Naira miliyan 11 a filin jirgin saman Sifen
An kama mahaifiyar Ronaldo da Naira miliyan 11 a filin jirgin saman Sifen

Jami’an tsaro sun cafke mahaifiyar Cristiano Ronaldo mai suna Dolores Abeiro da yunkurin barin kasar da Yuro dubu 45 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 11 da dubu 205 ba tare da an ba ta izinin yin hakan ba.

Rahoton da kafar sadarwa ta The Telegraph ta kalato ya nuna, mahaifiyar dan kwallon mai kimanin shekara 60, jami’an tsaro ne suka tsareta kuma suka binciketa a filin jirgin saman Barajas na Madrid kuma suka gano tana dauke da kudin a jakarta ta hannu da hakan ya saba wa dokar Sifen. Dokar Sifen ta nuna ba a amince ga wani ya bar kasar da kudin da suka haura Yuro dubu 10 kwatankwacin Naira miliyan 2 da dubu 490 baa lokaci guda ba. Rahoton ya kara da cewa, mahaifiyar tana kokarin tafiya Fotugal ne don ziyartar iyalanta da ke can, tun da ita da danta Ronaldo sun tare ne a Sifen a wani katafaren gida da ya gina musu tun bayan ya koma kulob din Madrid a shekarar 2009.
A kokarinta na komawa Fotugal kasar haihuwarsu ce ta gamu da wannan matsala bayan jami’an tsaron sun yi ram da ita a filin jirgin saman Sifen. Sai dai tuni jami’an tsaron suka kwace Yuro miliyan 35 daga cikin kudin kuma suka bar mata Yuro dubu 10 kacal kafin su barta ta fice daga kasar.
Sai dai kudin da ake tuhumarta ba kudin almundahana ko na sata ba ne kudi ne na kasahin kanta amma dokar kasar Sifen ce ta hana wani ko wasu fita daga kasar da kudin da suka zarceYuro dubu 10 ba tare da sun nemi izinin yin haka a lokaci guda ba.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram