An kama mahaukacin da ya mallaki Naira miliyan 1.5 a banki
jami’an tsaron farin kaya ta Sibil defens (NSCDC) a Jihar Ondo sun kama wani mutum da ake zargin yana daya daga cikin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da ke shigar mahaukata. Bayanai sun ce wanda ake zargin yana da kudi a asusunsa na banki da suka kai Naira miliyan 1 da rabi. […]
jami’an tsaron farin kaya ta Sibil defens (NSCDC) a Jihar Ondo sun kama wani mutum da ake zargin yana daya daga cikin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da ke shigar mahaukata.
Bayanai sun ce wanda ake zargin yana da kudi a asusunsa na banki da suka kai Naira miliyan 1 da rabi.
Kwamandan Hukumar NSCDC a Jihar Ondo, Mista Pedro Awili ya bayyana wa manema labarai cewa wanda ake zargin da kuma sauran mutum bakwai suna aikata wasu laifuffuka a Akure, babban birnin jihar.
Awili ya ce kama wanda ake zargin da laifin garkuwa da mutane, ya biyo bayan aiki wurjanjan da jami’an tsaro suka yi a birnin Akure. Ya kara da cewa, jami’an tsaron a ranar 15 ga Oktoba sun kama wani mutum mai suna Dele, wanda ke yin shigar mahaukata a yankin Isikan da ke Akure, dauke da wata wayar hannu, kirar Itel. Yayin da jami’an tsaron suke bincikar wayar tasa ce sai suka samu sakon an shigar masa da kudi a asusun bankinsa na Naira miliyan 1.5, inda bayan sun ga sakon shigar kudin, nan take mutumin da ake zargin ya kwace wayar ya fasa ta a kasa. Ya ce jami’an tsaron za su gyara wayar don su tabbatar da wanda ya tura masa kudin da kuma abokan aikinsa.”