An kama mai ƙera wa bata-gari makamai a Jigawa
Ya tabbatar mana da cewa ya kera makamai da dama kuma bai san adadin mutanen da ya sayarwa ba.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani mutum dan shekara 50, da take zargi da kera makamai a Karamar Hukumar Ringim.
Kakakin rundunar a jihar, mukaddashin sifuritendan ‘yan sanda Lawan Shisu ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis.
- NAJERIYA A YAU: Ta’adar Sakarwa Mata Ragamar Gida
- Da gaske Lalong zai ajiye kujerar Minista don karɓar ta Sanata?
A cewar Shisu, sun kama mutumin ne a ranar 16 ga watan da muke ciki.
“Rundunar ’yan sanda da hadin gwiwar ’yan sa-kai sun kama wanda muke zargi da kera wa bata-gari makamai a garin Yandutsen Kawari,” inji Kakakin ’yan sandan.
A binciken da aka gudanar a gidansa, an samu kananan bindigu biyu kirar gida, da kuma wasu manya biyu.
Shisu ya ce wanda suke zargin, da kansa ya tabbatar musu cewa yana kera makamai da dama, kuma sau tari bai san wadanda yake sayarwa ba.
SP Lawan Shisu ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.