An kama mai damfarar samar da guraben aiki a Kano
Akalla dai mata 10 ne suka yi ƙorafi a kan mutumin bayan ya karɓe musu kuɗaɗe
Rundunar Tsaro ta Sibil Difens reshen Jihar Kano, ta samu nasarar kama wani mutum da ake zargin ya ƙware wajen damfarar jama’a ta hanyar karɓar kuɗaɗensu domin samar musu ayyukan yi a hukumomin jihar.
Kakakin Rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.
Ibrahim Idris ya ce wanda ake zargin ya yi sojan gona, inda yake bayyana kansa a matsayin wani mai faɗa aji a jahar tare da nuna cewa yana da alaƙa da wasu hukumomin tsaro na ƙasar nan.
Akalla dai mata 10 ne suka yi ƙorafi a kan mutumin bayan ya karɓe musu kuɗaɗe da zummar zai samar musu aikin yi.
- Sojoji sun kashe gomman ‘yan bindiga a Filato
- Gwamnatin Nijeriya ta yi sakaci kan kisan Sarkin Gobir — Atiku
Wanda ake zargin ya amsa cewar haƙiƙa ya karɓi kuɗi sama da Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu (N1.2m) daga wurin matan.
Rundunar ta ƙara da cewa tuni jami’ansu da suke kula da binciken laifuka suka kammala bincike, inda kuma wanda ake zargin ya tabbatar da cewar ya ƙarbi kudaden, don haka za a gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.