An kama mai gadi ya fille kan gawa zai sayar
Mai gadin ya shirin sayar da kan gawar a kan kudi 50,000.
An cafke wani mai gadin dakin ajiye gawa bayan ya yanke kan gawar wani yaro domin ya sayar a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa shi jami’in kula da gawarwaki ne a cibiyar MABOD da ke Oke-Yidi, Abule Oloni, a Abeokuta.
- Karamar Sallah: An jibge jami’an tsaro 3,000 a Kano
- ’Yan sandan Isra’ila sun jikkata Falasdinawa 42 a masallacin birnin Kudus
Jami’an tsaron gwamnatin jihar Ogun na So-Safe ne suka kama shi a ranar Talata, “Bayan ya fille kan gawar wani karamin yaro a makabartar Oke Yidi da ke Abeokuta,” amma aka fafare shi aka kama shi, a cewarsu.
Kakakin rundunar S0-Safe, Moruf Yusuf, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da ake tuhumar shi.
Rahotanni sun bayanna cewa an kai gawar yaron makabarta ne daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Abeokuta, bayan ya mutu sakamakon cutar koda.
Wanda ake zargin ya ce, “Iyayen yaron da suka zo daga Ibadan sun nemi taimakona a matsayinsa na ma’aikacin ajiye gawa domin a binne gawar.
“Don haka na binne gawarsa a makabartar a gabansu da misalin karfe 7 na daren ranar Litinin.”
Sai dai a cewar kakakin na So-Safe, wanda ake zargin ya koma makabartar da misalin karfe 6 na safiyar Talata, ya sare kan gawar da nufin sayarwa.
“Daga baya wanda ake zargin ya amsa cewa wani Cif Ifalonishe wanda aka fi sani da Lanroye ne bukaci ya kai masa kan sabuwar gawa a kan N50,000.”
Kwamandan So-Safe, Soji Ganzallo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun mika wanda ake zargin ga ’yan sanda don fadada bincike.