An kama mai garkuwa da mutane a Kogi
Jami’an tsaro da ’yan banga sun kama mai garkuwa da mutane a Jihar Kogi
An kama wani mai garkuwa da mutane mai shekaru 43 a kauyen Ofodo da ke kusa da garin Egabada a Karamar Hukumar Igalamela-Odolu ta Jihar Kogi.
Jami’an tsaro da ’yan banga ne suka kama shi a ranar Litinin, inda suka same shi da bindiga tare da wasu abubuwa da ake tuhuma da suka hada da laya.
Wanda ake zargin dan asalin karamar hukumar Bida ne ta jihar Neja, a cewar shugaban ’yan banga a yankin, Mohammed Ajitata.
Mohammed ya ce dan bindigar ya amsa laifin, kuma ya yi zargin cewa wani mutum dan kauyen Shanawa da ke karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi ne abokin aikinsa.
- NAJERIYA A YAU: “Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000”
- Rikicin Isra’ila da Iran ne ya haddasa matsalar man fetur a Nijeriya — IPMAN
“Muna bin sa tun lokacin da muka gano motsin miyagun laifuka a unguwar Egabada-Odolu; ranar litinin, kuma muka ga kama shi a wani samame na hadin gwiwa,” in ji shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, wanda aka tuntube shi a kan lamarin ta hanyar sakon tes da kiran waya bai amsa ba.